<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Mu ƙanƙananan yara ne,
 Ba ƙarfi fa, ba gwaninta.
 Me za mu yi domin Yesu,
 Maɗaukaki, mai girma?

[V2]
 2) Mun sani masu tsarki
 Sun ba da ransu dominsa.
 Masu aminci, tsarkaka,
 Sun jure tsananin wuta.

[V3]
 3) Kaddararmu da tasu ɗaya,
 Mu kuwa muna yin wa'adi,
 Za mu bi su har mutuwa
 Don Yesu, haka za mu yi.

[V4]
 4) Kowace rana Masu Bi
 Wajibinmu ne za mu yi,
 Mu kashe mugun tunani,
 Mu hana aikin zunubi.

[V5]
 5) Loton da mu ke yin fushi,
 Ko mutane sun zage mu,
 Ko waɗansu sun dame mu,
 Ko alfarma ta cika mu,

[V6]
 6) A loton nan mu tuna fa,
 Mu amsa su da haƙuri,
 Maganarmu da ladabi
 Don yaƙin Ubangiji ne.

[V7]
 7) Murmushi na salama kuwa
 Ya haskaka fuskokinmu.
 Mu yi kome domin Yesu,
 Mu ƙaunaci jama'armu.

[V8]
 8) Kome ƙanƙantar yara fa,
 Sun iya ɗaukar giciyensu.
 Aikinsu daidai ƙarfinsu,
 Su yi kome domin Yesu</lyrics>
<title>Mu Ƙanƙananan yara ne LW310</title>
<hymn_number>310</hymn_number>
</song>